Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin rushe shugabancin hukumar kare haƙƙin masu saye ta jihar Kano wato consumer Protection Council.
A cewar sanarwar da sakataren gwamnatin Kano, Umar Faruk Ibrahim, ya fitar a Asabar din nan, matakin ya biyo bayan dogon rikicin shugabanci da hukumar ke fama da shi duk da ƙoƙarin sulhu da gwamnati ta yi.
Sanarwar ta ce an sallami shugaban hukumar, sakatare, da sauran dukkan mambobi, tare da umartar su, su mika dukkan kayayyakin gwamnati da takardu da ke hannunsu ga babban jami’in hukumar kafin jibi Litini.
Gwamnatin ta kuma bukaci su mika cikakken rahoton mika aiki ga ofishin sakataren gwamnati da na kwamishinan kasuwanci.
