
Gwamnatin Kano Ta Karɓi Ƙorafe-Ƙorafe Kan Malam Lawan Triumph ta mika lamarin ga kwamitin Shura na jihar
Musa Tanko, Sakataren Yaɗa Labarai na Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) ya sanar da hakan a wata takardar sanarwa da ya rarraba a kafafen yadda labarai na jihar a daren Alhamis.
Gwamnatin Kano za ta ɗau mataki kan Lawan Triumph
Sanarwar da ya sa hannu ta ce, ofishin ya karabi ƙorafe-ƙorafen sun fito daga kungiyoyin addinai guda 8 kan malamin.
Kungiyoyin su ne
1. Safiyatul Islam of Nigeria
2. Tijjaniya Youth Enlightenment Forum
3. Interfaith Parties for Peace and Development
4. Sairul Qalbi Foundation
5. Habbullah Mateen Foundation
6. Imaman Masallatan Juma’a na Qadiriyya
7. Kwamitin Malaman Sunnah, Kano
8. Multaqa Ahbab Alsufiyya
“SSG, a madadin gwamnati, ya umarci a mika duk ƙorafe-ƙorafen ga Kwamitin Shura na Jiha domin yin nazari mai zurfi tare da bai wa gwamnati shawarar da ta dace kan lamarin.” In ji sanarwar.
Gwamnatin Kano ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da kare zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna tsakanin dukkanin ƙungiyoyin addini a jihar.