
Hukumar Tace Fina Finai Da Dab’i ta Kano ta sanar da dakatar da wasu finafinai masu dogon zango
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a daren Lahadi.
Sauran finafinai da aka dakatar su ne:
- Dadin Kowa
- Labarina
- Gidan Sarauta
- Manyan Mata
- Dakin Amarya
- Kishiyata
- Garwashi
- Jamilun Jiddan
- Mashahuri
- Wasiyya
- Tawakkaltu
- Mijina
- Wani Zamani
- Mallaka
- Kudin Ruwa
- Boka Ko Malam
- Wayasan Gobe
- Rana Dubu
- Fatake
- Shahadar Nabila
- Tabarmar
- Rigar Aro
Sanarwar ta ce, shugaban hukumar Abba El-mustapha ya dauki matakin ne domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ka’idar doka ba.
Jami’in ya kuma ce a shirye suke su gurfanar da duk wanda yayi kunnen kashi da wannan umarni gaban kotu domin fuskantar hukunci dai dai da laifin da ya aikata