Gwamnatin Kano ta ba da umarnin bibiyar batun yaran jihar da aka kama a zanga zanga

0
180

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinan shari’a na Kano, Barista Haruna Isa Dederi, da ya gaggauta duba batun yaran nan yan asalin jihar Kano da aka gurfanar da su gaban babbar kotun tarayya sakamakon zanga zangar tsadar rayuwa ta watan Agusta.

Ta cikin wani saƙo da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce hankali ya kai kan yaran masu karancin shekaru, wadanda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido wajen ganin an tauye musu haqqi na rayuwa ba

Ya ce maimakon hakan za su dauki dukkan matakan da suka kamata wajen ganin yaran sun samu yanci.

An kama waɗanda ake zargin ne a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a faɗin Najeriya tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

An kama su ne a jihohin Kano da Katsina da Gombe da Abuja da Jos da kuma Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!