Gwamnatin Kano ta bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga mutanen da ibtila’in fashewar tankar mai ya shafa a jihar Jigawa

0
296

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga mutanen da ibtila’in fashewar tankar mai ya shafa a garin Majiya dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.

Gwamnan ya bayar da tallafin ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar jihar Jigawa bisa ibtila’in da ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 170 da kuma jikkata al’umma da dama.

Ya mika ta’aziyyarsa a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano tare da fatan Allah ya kare afkuwar hakan a nan gaba.

Gwamnan ya kara da cewa, ibtila’in ba iya al’ummar jihar Jigawa ya shafa kadai ba, har ma da al’ummar jihar Kano, la’akari da dangantakar dake tsakanin jihohin biyu.

Daga nan ya yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda suku rigamu gidan gaskiya, ya kuma bawa wadanda suka jikkata lafiya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa a nasa bangaren, gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi Danmodi ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ziyarar jaje da ta’aziyya da ya kawo wa al’ummar jihar inda ya ce ziyarar zata kara karfafa dangantakar dake tsakanin jihohin biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!