Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin Kano ta ce zata cigaba da karfafawa ma’aikatu da hukumomin gwamnati gwiwa ta hanyar samar musu da kayan aiki.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Sulaiman Wali Sani, ne ya bayyana haka yayin raba motoci da babura ga ma’aikatun gwamnati ranar Litinin.
Ya ce wannan na daga cikin burin gwamnatin Kano na karfafawa ma’aikatu domin yin aiki yadda ya kamata.
Ya ce wannan somin tabi ne za a cigaba da samar da karin kayan aiki ga hukumomi da ma’aikatun gwamnati.
An raba motoci kirar Hilux da hummer Hiece fiye da 20 da babura 15 ga ma’aikatu da hukumomi daban daban.
Cikin motocin akwai na asibiti guda 2 inda daya za a barta a gidan gwamnati daya kuma za a baiwa asibitin Nuhu Bammali.
Da yake jawabi Dr Aliyu Isah Aliyu, daga hukumar Kididdiga ta jihar Kano, ya ce zasu yi amfani da motocin da aka basu yadda yakamata musamman bibiyar aiyuka da tarukan jihar Kano.
Ya ce zasu tabbatar da cewa sun kula da motocin yadda yakamata.
Misbahu Muhd Fada, daya ne daga cikin jagororin kungiyar Hisba ta jihar Kano wadanda suka rabauta da babura 15 ya ce zasu yi amfani da baburan wajen shiga lungu da sako dan magance aikata badala.
Shi kuwa shugaban hukumar tace fina finai ta jihar Kano Abba Mustapha, ya ce sun rabauta da motoci biyu Kuma zasu taimaka musu wajen aiyukansu.
Ya ce zasu cigaba da aiki don tsaftace harkar fina finai da bunkasa su a jihar Kano.
