

Gwamnatin kasar Ghana ta buƙaci ma’aikatan lafiya da ungozoma da ke yajin aiki tun ranar 2 ga Yuni da su janye yajin aikin wanda yanzu ya shiga mako na biyu.
Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Ghana, Farfesa Samuel Kaba Akoriyea ne ya bayyana haka, yana mai cewa yajin aikin na haddasa cikas sosai ga tsarin kula da lafiyar al’ummar ƙasar.
Yajin aikin ya ƙara ta’azzara ne a ranar Litinin lokacin da ma’aikatan suka janye ayyukansu gaba ɗaya daga cibiyoyin lafiya, wanda hakan ya jefa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya cikin rudani da cunkoso da kuma gazawa.
Gwamnatin ta roƙi ma’aikatan da su yi sassauci tare da janye yajin aikin domin ceton rayukan marasa lafiya da ke cikin matsanacin halin, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yadda za a shawo kan batun
Rahotannin sun bayyana cewa yajin aikin ya samo asali ne tun bayan da ma’aikatan lafiya na kasa suka nemi gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka na kara musu albashi,