Gwamnatin jihar Bauchi zata hada hannu da kwamfanoni masu zaman kan su domin samar da ayyukan yi ga al’umma da kuma inganta harkokin tsaro a jihar.
Gwamna Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ne ya bayyana hakan, a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan kamfanonin samar da siminti wadanda zasu hada hannu da gwamnatin jihar.
Ya kara da cewa, samar da kamfanonin a jihar ta Bauchi zai taimaka wajan dakile dukkanin wata barazanar rashin tsaro.
Sanata Bala Muhammad ya ce kamfanonin samar da simintin zasu dauki matasan jihar ta Bauchi sama da guda dubu biyu domin basu aikin yi.
Wakilin mu Ibrahim Aminu Rimin kebe ya rawaito mana cewa, gwamnan jihar ta Bauchi ya bada tabbacin hadin kan gwamnati wajan ganin shirin ya samu nasara.
