
Gwamnatin Sokoto ta sanar da shirinta na sanya masu hakar kabari cikin tsarin albashi tare da gina karin makarantun islamiyya.
Gwamnan jihar Ahmad Aliyu ne ya bayyana haka cikin sanarwar da daraktan yada labaransa Abubakar Bawa, ya fitar a ranar Juma’a, yayin bude masallacin juma’a da ajujuwan islamiyya a kauyen Kirare a karamar hukumar Goronyo.
Gwamman Ahmad Aliyu ya ce, za a sanya su cikin tsarin albashi duba da irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma
Ya kuma ce an bayar da kwangilar gyara masallatai 65 a jihar kuma masallacin Kirare shine na 16 da aka kammala.
A jawabin sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya yabawa gwamnan bisa gyarawa da gina masallatai da yake yi.