Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce zai ɗauki matakin daya dace ga duk kwamishinan da ya yi wasa da aikinsa na gwamnati.
Alhaji Abba Kabir ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar zartarwa karo na 23 da aka gudanar a gidan gwamnati yau Laraba.
Gwamna Yusuf ya ce a wannan lokaci da ake ciki ba zai lamunci duk wani sakaci ba, dan haka duk kwamishinan da ya kawo wasa zai ɗauki matakin da ya kamata akan shi.
Ya ja hankalin sababbin kwamishinoni da ya nada da su haɗa kai da sauran kwamishinoni tare da aiki guri guda domin ciyar da jihar Kano gaba.
Yayin zaman majalisar zartarwar gwamna Abba Kabir ya kuma bayyana wasu shirye-shiryen da gwamnatin shi zata gabatar nan bada jimawa ba.
Wasu daga cikin ayyukan da gwamnati zata gabatar sun haɗa da biyan wasu daga cikin ‘yan fansho hakkokinsu su da za ayi ranar Alhamis na Naira Bilyan Biyar dan tabbatar da alƙawarin da suka ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe.
Haka zalika gwamna ya kuma bayyana shirin gwamnatin sa na bada kayan makaranta kyauta ga ɗaliban ajin farko.
“Muna sanar muku da shirye-shiryen mu masu yawa da muke dasu nan da Kwanaki Kaɗan masu zuwa na wannan sabuwar shekarar.”
“Muna kuma bada tabbacin nan da watanni uku masu zuwa zamu gina matsakaitan gidaje da zasu laƙume kimanin naira bilya 10 ga waɗanda ruwa ya yi masu ɓarna in Allah ya yarda.”
Wakilin mu Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa gwamna Kanon yace wasu daga cikin abubuwan da suka faru a cikin kwanaki kaɗan na ƙarshen shekara da ta gabata sun haɗa da dawowar ɗaliban Jihar Kano daga Ƙasar Indiya bisa ƙaro ilimin digiri na biyu da gwamnati ta tura su.Haka kuma gwamnan ya kuma kara miƙa saƙon shi na godiya ga majalisar dokokin Jihar Kano bisa haɗin kai da suke baiwa ofishin shi na fatan samun nasarar shi a gwamnatance.