Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya gidan rediyon Premier Radio murnar cika shekaru huɗu da kafuwa. Ya kuma jinjiwa shugabanta Abba Dabo da kafa gidan da kuma jagoranci na gari.
Gwaman Abba Kabir ya bayyana gidan rediyon a matsayin wata kafa mai inganci da kwararrewa a fannin watsa shirye-shirye da ke bayar da gudunmawa mai muhimmanci ga wayar da kan jama’a da kuma inganta shugabanci na gari a Jihar Kano.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Mai Magana Da Yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi,
“Premier Radio ta samu amincewar jama’a ta hanyar bayar da labarai marasa son zuciya, ba da dama ga ra’ayoyi daban-daban, da kuma kiyaye ka’idojin adalci da rikon amana a fannin watsa shirye-shirye.
“Gidan rediyon ya taka rawar gani wajen inganta zaman lafiya, hadin kai, da kuma tattaunawa mai fa’ida a tsakanin jama’a, yayin da yake zama ingantaccen dandamali na shigar da ‘yan kasa cikin al’amura ba tare da nuna bambancin siyasa, kabilanci, ko yanki ba”. In ji sanarwar.
- Premier Radio Ya Kafa Tarihin Samun Mabiya 1M A Facebook
- Yau Premier Radio ke cika shekara 4 cif-cif
Gwamna Yusuf ya kuma taya Shugaban Gidan Rediyon, Malam Abba Dabo, murnar shugabancinsa mai hangen nesa da kuma ci gaba da zuba jari a aikin jarida mai inganci.
Sannan gwamman ya yi fatan Premier Radio za ta ci gaba da bunkasa, kasancewa mai muhimmanci, da kuma yin tasiri.
Ya kuma sake jaddada goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano ga kafafen yada labarai da ke inganta gaskiya, rikon amana, da kuma amfanin jama’a.
