Gwamnan Kano ya amince da naɗin Farfesa Amina Salihi Bayero, a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar Northwest mallakin jihar.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, Kakakin gwamnan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
“Gwamna ya amince da naɗin ne bayan tantancewa da kwamitin gudanarwar jami’ar ya yi mata a matsayinsa na jagoran jami’ar”. In ji Kakakin a cikin sanarwa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa shugaban kwamitin da mambobinsa kan jajircewarsu wajen bin ƙa’idojin tantancewar.
Gwamnan ya nemi a yi mata addu’ar samun nasara wajen gudanar da jagorancin Jami’ar.
Naɗin Farfeasa Amina zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamban 2025, har zuwa tsawon shekaru biyar.
Farfesa Amina Salihi Bayero ƙwararriya ce a fannin ilimin Sinadarai, musamman Ilimin nazari da binciken Sinadarai, kuma ita ce mace ta farko da ta samu digiri na uku a wannan fannin daga Jami’ar Bayero Kano.
Farfesa Amina ta taɓa riƙe muƙamai da dama a harkar ilimi da gudanarwa, ciki har da shugabar sashen Ilimin Sanadarai, da kuma Mataimakiyar Shugabar Jami’a, a Jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Ana girmama Farfesa Amina saboda jajircewarta wajen horar da matasan masana kimiyya.
