
Gwamnan Kano Abba Kabir ya ce gwamnatinsa ta kaddamar da shirin kiwon dabbobi na ₦2.3 biliyan tare da raba awaki 7,158 ga mata 2,386 a kananan hukumomi 44.
Ya bayyana haka yayin bikin cikar kasar nan shekaru 65 da samun ‘yancin kai ranar Laraba.
Ya ce gwamnati ta baiwa masu digiri 1,130 kayan koyon sana’o’i domin dogaro da kansu.
Yayin da aka baiwa dubban masu ƙananan sana’o’i naira dubu ₦50,000 kowanne a matsayin jari.
Abba Kabir ya ce don farfado da aikin gona, gwamnati ta raba takin zamani kyauta wanda ya kai darajar biliyan 1 ga manoma ƙanana 52,800 kuma ta kaddamar da aikin ban ruwa na biliyan 16 biliyan a Dam din Jakara.
Ya kara da cewa, aikin ci gaban noma da kiwo na Jihar Kano (KSADP) ya tallafawa manoma sama da 477,000.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa na sabunta birane ciki har da gyaran tituna 17 da suka lalace a cikin birnin Kano da kuma sanya naira biliyan 27 ga manyan hanyoyi.
Ya kuma dawo da ayyuka a Gidan Ruwa na Tamburawa da kuma sayen karin injinan famfo don kara yawan samar da ruwan sha.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara biyan bashin naira biliyan 48 na fansho da garatuti da ba a biya ba, wanda daga ciki an riga an fitar da naira biliyan 27.