
Gwamnan Kano ya kaddamar da aikin Titin Zungeru a unguwar Sabon Gari.
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan jihar Kano Al Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da sake gina titin Zangeru dake unguwar Sabon Gari a karamar hukumar Fagge.
Titin na Zangeru na daya daga cikin manyan titunan jihar Kano guda 17 wanda gwamna ke aikin sabuntawa Kano.
An bayar da aikin mai nisan kilomita 3.6 tun a wa’adi na biyu na mulkin tsohon gwamna Kwankwaso sai dai bayan barinsa mulki akayi watsi da aikin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce Titin na Zungeru wani bangare ne na kokarin gwamnati na samar da aiyuka don inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Ya bukaci Dan kwangilar dake aikin da ya tabbatar ya kammala shi akan lokaci.
Ya ce aikin Titin mai hannu biyu zai bunƙasa tattalin arziki, harkokin kasuwanci, da kuma rage cinkosan ababen hawa.
Ya yaba da goyan baya da hadin kan da al’ummar Sabon Gari suke baiwa gwamnatin sa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano su cigaba da dabbaka zaman lafiya a jihar Kano.