Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jajantawa al’ummar karamar hukumar Rano da rundunar ‘yan sandan Kano bisa rikicin da yakai ga mutuwar wani matashi da Baturen ‘yan sandan yankin.
Gwamnan ya mika wannan jaje ne yayin kaddamar da sake gina Titin Zungeru a unguwar Sabon Gari da yammacin ranar Talata.
Gwamnan ya ce ana sane da cewa lamarin ya samo asali ne bayan da aka kama wani matashi wanda yayin bincike ya rasu a hannun ‘yan sandan Rano sakamakon duka.
Ya ce hakan ne ya tunzura matasa suka dauki doka a hannu wanda sakamakon haka DPO ya samu raunuka bayan kai shi asibiti aka tabbatar da mutuwar sa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, yayi kira ga al’ummar Kano musamman matasa su guji daukar doka a hannu maimakon haka su rinka barin jami’an tsaro su yi aikin su.
Ya ce sake rasa rayuwar wani mutum wani al’amari ne mara dadi.
Ya ce a matsayin su na shugabanni basa son zubar da jini ko rasa ran wani musamman matasa.
