Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bude titi mai tsawon kilo mita 5 tare da fitilu masu amfani da hasken rana a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Gwamnan yace amfara aikin tun lokacin gwamnatin Senator Rabiu Musa Kwankwaso a shekarar 2012 wanda gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje tayi watsi da shi.
Abba Kabir ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda aka kammala aiki cikin nasara.
Ya kuma jaddada kudirin gwamantinsa na ci gaba da kammala dukkan aiyyukan tituna masu tsawon kilo mita biyar a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Gwamnan na Kano ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da aikace aikace na ci gaba a karamar hukumar ta Dawakin Tofa.
Wakilinmu Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa yayin kaddamar da titin, karamar hukumar Dawakin Tofa ta karrama gwamna Abba Kabir Yusuf da kyautar doki.