
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin ci gaba da aikin titin Janguza zuwa Kabo zuwa Karaye wanda aka dakatar na tsawon lokaci.
Wannan mataki na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar bayan ziyarar gaisuwar Sallah da Sarkin Karaye ya kai wa Gwamnan a ranar Alhamis.
Titin Janguza zuwa Kabo zuwa Karaye an fara shi ne tun zamanin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso amma bai samu kammala ba tsawon shekaru takwas na mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta sake duba kwangilar tare da bayar da duk wasu takardu da suka dace don tabbatar da ci gaba da aikin cikin gaggawa.
A cewar sanarwa, mai martaba Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, ya bayyana kudirin masarautar na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma, a jawabinsa.
Sarkin ya kuma yaba wa yunƙurin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi wajen habaka jihar Kano ta fuskar ayyukan raya kasa.
Wannan matakin ya nuna kokarin gwamnatin Kano na tabbatar da ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su amfani al’umma, tare da mayar da hankali kan ci gaba mai dorewa a fadin jihar.