Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar kaduwarsa da alhini bisa rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Gwamnan ya bayyana shi a matsayin fitaccen mutum wanda rayuwarsa ke cike da ɗa’a, gaskiya, da ƙauna ta ga Najeriya.
A cikin saƙon ta’aziyya, Gwamna Yusuf ya yabawa rayuwar marigayi Shugaban Ƙasar, yana mai cewa ko a matsayinsa na mulkin soja da matsayinsa na zababben shugaban ƙasa, Buhari ya sadaukar da rayuwarsa wajen haɗin kai, daidaito, da cigaban ƙasa.
Ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya sadaukar da duk rayuwarsa wajen hidimtawa ƙasar nan da jarumtaka da gaskiya.
Ya kara da cewa Jajircewarsa, sauƙin hali, da kishinsa ga walwalar talakawa za su ci gaba da zama abin koyi ga al’ummomi masu zuwa.
Gwamnan ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayi Shugaban Ƙasa, gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina, da kuma daukacin ‘yan Najeriya da ke jimamin wannan babban rashi.
Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa marigayin, ya jikansa da Aljannatul Firdaus, ya kuma ba ƙasa ƙarfin hali da juriyar ɗaukar wannan babban rashi.
