Gwamnan ya mika ta’aziyar ne yayin zaman majalisar zartaswar a gidan gwamnatin Kano karo na 34 ranar Alhamis.
Abba Kabir Yusuf ya ce rasuwar fitaccen malamin babban rashi ne ga al’ummar musulmi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa tare da bai wa iyalansa hakurin jure rashin sa.
