Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya nuna takaicin sa kan yadda gwamnatin Ganduje ta cefanar da Ganuwar Kano.
Ya bayyana haka yayin bikin ranar Al’adu ta duniya da akayi a dakin taro na Coronation dake Gidan Gwamnatin Kano ranar Lahadi.
Ya ce abin bakin ciki bayan shudewar gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso aka cefanar da Badala.
Ya ce duk mai tafiya daga gidan Murtala zuwa Kofar Kabuga zai ga yadda aka lalata Badala aka sassare ta aka baiwa mutane suka yi kantuna ba tare da la’akari da Al’ada da Tarihi ba.
Ya ce abin bakin ciki ne Kuma sun dakatar da yin gine-ginen.
Gwamna Abba Kabir ya ce duk da ƙasar Jamus ta shigo domin gyara Badalar amma gwamnatin da ta gabata bata bayar da hadin kai ba.
Gwamnan na Kano ya ce gwamnati zata mayar da Gidan Yarin Kurmawa zuwa cibiyar Nazarin Al’adun Gargajiya inda za a mayar da kurkukun zuwa Janguza.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da wadanda suka gaji sana’o’in Gargajiya su rike su yadda ya kamata.
Ya ce zasu basu hadin kai da farfado da sana’o’i da aladun Gargajiya.
Ya ce sun bayar da kwangilar gyara marina dake Kofar Mata da Karofin Sudan.
Abba Kabir Yusuf, ya ce sun bayar da kudi don gyara dukkan kasuwanni musamman inda ake sayar da kayayyakin Gargajiya.
