Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar shirin l dashen bishiyu miliyan biyar da rabi.
An kaddamar da shirin a karamar hukumar Makoda ranar Lahadi a wani mataki yaki da dumamar yanayi da kare muhalli a fadin jihar Kano.
Da yake jawabi Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce shirin wani bangare ne na tabbatar da ingantaccen muhalli da yaki da illolin canjin yanayi da ke barazana ga lafiyar al’umma da amfanin gona.
Ya ce dashen bishiyun hanya ce mafi sauki kuma mai amfani wajen dakile fari da kuma bunkasa ingancin iskar da ake sha.
Gwamnan ya kuma bukaci jama’a su bada hadin kai wajen kula da bishiyun da za a dasa, yana mai cewa gwamnati za ta samar da kayayyakin kula da su da kuma horar da masu ruwa da tsaki a lamarin.
A nasa jawabin kwamishinan Muhalli, Dahiru Hashim, ya ce an samar da irin bishiyun a gida jihar Kano.
Ya ce bishiyun da aka dasa zasu taimaka wajen magance kwararowar hamada da inganta iska da Muhalli.
Dahiru Hashim ya yabawa masu ruwa da tsaki da gwamnan Kano bisa gudunmawar su wajen samun nasarar shirin.















