
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da kyautar motoci ƙirar Hilux guda shida da babura 30 domin taimaka wa sojoji wajen yaƙi da ’yan bindiga a faɗin jihar.
Gwamnan, ya miƙa motocin da baburan ga Kanal Hussaini Rabi’u Toro na rundunar sojoji ta takwas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Ya ce wannan kyauta na cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da walwalar al’umma.
Ya ƙara da cewa, an fara bai wa sojoji ne kyautar, amma sauran hukumomin tsaro su ma za su samu irin wannan tallafi nan ba da jimawa ba.
Da yake bayani a wajen taron, Kanal Hussaini Toro, ya gode wa gwamnan bisa wannan taimako, inda ya cewa hakan zai ƙara musu ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.