
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusif ya umarci masarautun jihar Kano hudu su fara shirye shiryen gudanar da hawan sallah karama.
Umarnin na zuwa ne bayan an shafe wani lokaci ba a gudanar da hawan ba saboda rahotannin barazanar tsaro da rundunar ‘yan sanda ke samowa.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a jawabinsa ga sarakunan yayin bude baki da su a gidan gwamnatin jiha, a ranar Talata da dare.
Ya kuma ce jami’an tsaro za su tabbatar da bayar da tsaron da ya kamata don tabbatar da an yi hawan cikin lumana.
Sannan ya sanar kaddamar da majalisar Sarakunan jihar a watan Afrilu da kuma dukkanin dokoki da yadda majalisar za ta tafi da aikinta sai a ranar kaddamar da ita zai bayyanar da su.
A nasa jawabin shugaban majalisar sarakunan kuma sarkin Kano Muhammad Sunusi II ya tabbatar da cewa dangantaka tsakaninsa da sauran sarakuna masu daraja ta biyu zata ci gaba da zama abar kwatance wajen aiki yadda ya kamata don ci gaban alumma.

Sarkin Karaye, Muhammad Muhammad Maharaz; da sarkin Rano Amb. Muhammad Isa Umaru; da sarkin Gaya, Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, sun nuna jin dadinsu a madadin alumma kan wannan mataki da gwamnan ya dauka.