
Gwamna Yusuf ya bada umarnin ne a lokacin da ya kai ziyara garin na Rimin Zakara a ranar Alhamis.
Ya ce, ya zama wajibi a dakatar da rusau din domin kare rayuwakan jama’a da dukiyoyinsu.
Gwamnan ya kuma ci alwashin kawo karshen turka-turka tsakanin mazauna garin da kuma Jami’ar Bayero tsawon sama da shekara 30 da ya haifar da rikicin
Sannan ya bada umarnin a gina babban masallacin Juma’a a garin domin sadaukarwa ga wadanda suka mutu.
“Wadanda suka jikkata kuma, gwamnatin Kano za ta ci gaba da Kula da su”. Inji shi.
Gwamna Yusuf ya kuma yi alkawarin samar da ayyukan raya kasa a garin na Rimin Zakara.
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya Kai irin wannan ziyarar a inda ya jajanta wa mutanen garin tare alkawarin shiga tsakanin.