
Ahmad Hamisu Gwale
Fagen siyasar jihar Jigawa na fuskantar sabon salo ganin yadda Gwamna Umar Namadi ya fara bayyana goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Wannan yanayin ya janyo ce-ce-ku-ce ga siyasar jihar duba da cewa sauran sassan jihohin Arewacin Najeriya tuni suka yi nisa wajen nuna shahadarsu ga tafiyar siyasar shugaba Tinubu wajen maimaitawa a karo na biyu.
Sai dai wannan yanayi ya sauya tun bayan da magoya bayan Ministan tsaron kasar nan, kuma tsohon Gwamnan jihar suka maida hankali wajen tallata manufofin Gwamnatin shugaba Tinubu.
Lokaci zuwa lokaci ana ganin magoya bayan Ministan tsaron wajen bayyana inda Gwamnatin tarayyar ta sa gaba ta fuskar fito da ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma da Tinubu ke yi.
Yanayin dai ya fara zama wanda a iya cewa Gwamna Namadi da magoya bayansa basa jin dadin faruwarsa, wanda tuni Gwamnan yayi mi-ara koma baya a wani taron gangamin al’ummar da ya wakana a karamar hukukar Roni ta jihar, inda Gwamnan ya bi sahun magoya baya wajen rera wakar ‘Omologo’ da aka yiwa shugaba Tinubu a wani mataki na bayyana goyon baya.
Tuni dai masu sharhi kan al’amuran siyasar jihar ke cewa Gwamnan ya bi tsarin tafiyar shugaba Tinubu dari-bisa-dari kasancewar wannan shi ne karo na farko da aka hango shi a bainar jama’a da wannan yunkurin.
Har ila yau sun kara da cewa hakan na alamta Gwamna Namadi baya son a bar shi a baya wajen nuna goyon baya da tsarin Gwamnatin ta su mai mulki ta APC.
Sabon gangamin nuna biyayya na iya zama abin son kai fiye da gaskiyar lamarin abin da yake a zahiri. Wanda ke nuna cewa watsi da siyasar Tinubu a cewarsu, zai iya zama barazana ga Namadi a matakin ƙasa, alhali rungumar shi zai tabbatar da ci gaba da wanzuwarsa a siyasar jihar da ta kasa baki daya.
A halin yanzu, sakon ci gaba da tallata siyasar jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Jigawa na ci gaba da samun goyon baya tun bayan hobbasa da shugabannin siyasar jihar ke yi, wanda ka iya zama babban matakin kai ga nasarar tazarcen Tinubu a kakar zaben shekarar 2027.