Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamari ya haifar da damuwa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar noma, musamman manoma da ke fargabar cewa ci gaba da faduwar farashin kayan amfanin gona na iya sa wasu su hakura da harkar noma.
Saboda hauhawar farashin kayan abinci a wadannan shekarun, manoma da dama sun samu riba mai yawa, wanda hakan ya sa noma ya zama abin sha’awa.
Sai dai faduwar farashin kayan abinci a kwanan nan ya haifar da mabanbanta ra’ayoyi, inda masu saye ke jin sassauci, manoma na fargabar asara, ganin cewa sun sayi kayan noma a farashi mai tsada.
A cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS, hauhawar farashin abinci ya ragu kadan a watan Disamba 2024, daga kashi 39.93% zuwa 39.84%.
A sabuwar kididdigar da NBS ta fitar kwanan nan, hauhawar farashin abinci ya ragu zuwa kashi 26.08% a watan Janairu.
