
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da Majalisar Shura ta jihar domin tallafa wa gwamnati da shawarwari kan batutuwan da suka shafi gyaran tarbiyya da kyautata dabi’un al’umma.
A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamna, Mustapha Muhammad ya fitar, an kafa wannan majalisa ne domin ta zama wata hanya ta haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin addini wajen yaki da munanan dabi’u da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa babban burin majalisar shi ne tunkarar matsalolin da suka addabi matasa a jihar, musamman shaye-shaye da ayyukan ta’addanci, tare da jagorantar su zuwa hanya madaidaiciya.
Ya kuma buƙaci majalisar da ta shawarci Limaman Juma’a su rika gabatar da hudubobi masu jaddada zaman lafiya da haɗin kai tsakanin jama’a, domin ƙarfafa ɗabi’un kirki da ƙaunar juna.
Majalisar ta kunshi wakilai daga manyan ƙungiyoyin addini na Musulunci da Kiristanci a jihar, domin tabbatar da wakilci da fahimtar juna tsakanin mabambantan bangarori.




A nasa jawabin yayin kaddamar da majalisar, Wazirin Kano, Sheikh Sa’ad Shehu, ya gode wa Allah bisa wannan dama, yana mai jaddada cewa aikin da ke gaban su babba ne, kuma suna fatan samun taimakon Allah wajen cika shi yadda ya dace.