Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tura sunan Comrd. Saʼidu Yahya ga majalisar dokoki domin tantancewa da tabbatar da shi a matsayin shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta Kano.
Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a daren jiya Alhamis.
Sanarwar ta ce, Comrd. Saʼidu Yahya kwararren jami’i ne da ya shafe fiye da shekara 18 a harkokin yaƙi da rashawa.
Ya yi aiki a hukumar ICPC, inda ya rike mukamai da dama a fannin bincike, gano kadarori da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati da ‘yan siyasa.
Gwamnan ya ce ƙwarewar Yahya a bincike da bin sawun kadarorin da aka samu ta hanyar cin hanci za ta ƙara wa hukumar ƙarfin yakar rashawa a Kano.
Idan har majalisar dokokin Kano ta amince, to Sai’du Yahya zai maye gurbin Zahradden Kofar Mata wanda aka nada mukaddashin shugaban hukumar, bayan Muhyi Magaji Rimin Gado ya kammala wa’adinsa na shugabantar hukumar ta Anti Corruption.
