Gwamantin Nigeria ta karyata sabon zargin shugaban kasar Niger Abdurrahaman Tchiani game da cewa ya fadawa gwamnatin Nigeria cewa kasar faransa na kokarin kafa sansanonin yan ta’adda a Arewa masu Yammacin kasar.
Hakan na cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan yada labarai da sadarwa ga Ministan Harkokin Wajen kasar Alkasim Abdulkadir ya fitar.
Sanarwa ta kuma kara da cewa Zargin da shugaba Tchiani ya yi a wata hira da yayi da gidan wani talabijin a babban birnin kasar Yamai na ranar Kirsimeti ba gaskiya bane ce kuma yaudara ce. Babu sansanin “kasar Kanada” da sojojin Faransa ke da sansani a jihar Borno.
Abu mafi muhimmanci shi ne, babu wani sojan Faransa a Najeriya ko wani shiri da gwamnatin Najeriya ke yi na kafa ofishin soja da Faransawa ke rike da su inji sanarwar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa Shugaba kasar Nigeria Bola Ahmed Tinubu ya kasance a birnin Paris, inda Najeriya da Faransa suka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin biyu na bunkasa ababen more rayuwa da samar da abinci.
Yarjejeniyoyin sun kuma hada da shirin zuba jari na Euro miliyan 300 don tallafawa muhimman ababen more rayuwa, na kiwon lafiya, sufuri, noma, makamashi a fadin Najeriya. Don haka ba a musanya kudaden don kafa sansanonin soja ba.
Har ila yau, muna sake nanata babu wani sabani a cikin dangantakar Najeriya da Faransa.
Yana da kyau a bayyana cewa a ko da yaushe alakar Najeriya da Faransa tana da kyau, kuma suna mutunta juna, da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na juna