Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya jajantawa rukunin masana’antu na Dakata da Gobara ta shafa.
Gwamnan yayi wannan jaje ne yayin ziyarar da ya kai rukunin masana’antun ranar Asabar.
Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin Kano ta basu tallafin naira miliyan 100 kuma za a sanya musu wutar Solar.
Ya ce amadadin Gwamnati da al’ummar Kano suna jajantawa ‘yan kasuwar.
Ya kara da cewa kasuwar tana tallafawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Kano da magance zaman kashe wando a tsakanin matasa.
Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga manyan mutane da ‘yan kasuwa a Kano da Najeriya su tallafawa wadanda gobarar ta shafa.
Ya ce akwai bukatar a tallafa musu ba wai iya jajantawa a jaridu ba.
Ya ce gwamnatin Kano zata taimake su wajen farfado da masana’antun.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin share kasuwar ta yadda za ayi saurin farfado da kamfanoni da injinan da suka kone.
Ya ce za a yi taswira domin mayar da gurin na zamani ta yadda ba za a kara samun makamanciyar gobarar ba.
Abba Kabir, ya ce gwamnatin Kano zata bude asusu ga wadanda suke son tallafawa mutanen dake rukunin kananan masana’antun na unguwar Dakata.
