Shugaba Tinubu ya sake Buba Marwa a matsayin Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA a tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai ya fitar a ranar Juma’a.
Marigayi Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Buba Marwa a muƙamin a watan Janairun 2021.
Marwa ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi daga shekarar 2018 zuwa Disamba 2020.
Sabon nadin na nufin tsohon hafsan soja dan asalin jihar Adamawa zai ci gaba da rike mukamin har zuwa shekarar 2031.
Marwa ya taba zama gwamnan soja na jihohin Legas da Borno, ya kammala karatu a Makarantar Soja ta Najeriya da kuma Kwalejin Tsaro ta (NDA).
Bayan ya zama cikakken soja a shekarar 1973.
