
Motar da ta karya shingen da hakan ya ji wa 'yan makaranta ciwo
Daga Khalil Ibarahim Yaro
Wani direban motar daukar kaya ya karya shingen KAROTA na hana manyan motoci bin hanya, ya kuma ji wa kansa da kuma wasu yara ‘yan makaranta ciwo.
Lamarin ya faru ne a yammacin Litinin a titin zuwa gidan gwamnatin Kano, State road daidai fitilar bayar da hannu a mahadar titin da Audu Bako da ake kira ‘Danjar Magwan.
Jami’in hukumar KAROTA Sale Ubale Minjibir da wakilinmu ya taras a wurin ya dora laifin abin da ya faru ga taurin kan Direban na bin hayar da aka sa shingen da cewa motar za ta wuce.
“Tun kafin ya shigo aka ce masa kar ya shigo, amma ya shigo ya haifar da wannan hasara. Kana gani karfen ya karye. … karfen ya rabu daga inda aka kafa shi.” in ji Jami’in.
Dangane da wadanda suka jikkata sakamakon hadarin, Jami’in ya ce, direban motar ne da kuma wasu yara ‘yan makaranta guda biyu, da cewa a lokacin da aka sanar da su, suka kuma zo wurin ba su taras da su ba an garzaya da su asibiti.