Gwamnatin Kano ta zargi tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da janyo cutar mashako ta Diphtheria jihar Kano.
Gwamnatin ta yi zargin ne ta bakin Kwamishinan lafiya na jihar Abubakar Labaran Yusuf, a yayin bikin sake kaddamar da shirin kula da mata da kananan yara da aka gudanar a ranar Litinin, a Karamar Hukumar Kumbotso.
“A lokacin da muka karbi mulki mun gano gwamnatin Ganduje ta yi watanni 18 ba tare da ta yi allurer rigakafin yara ba. Wannan ne yasa jihar Kano ta yi ta fama da cutar Diphtheria.” Inji shi.
Kwamishinan Lafiyar ya Kuma koka kan yadda gwamnatin Abbdullahi Ganduje ta yi watsi da bangaren kula da cimaka ta yara a asibitocin jihar Kano.
Abubakar Labaran Yusuf, ya Kuma ce gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amincewa ma’aikatar lafiya naira miliyan 176 domin gyara dakunan cimakar na asibitocin jihar.