
Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) ta ɗauki sabbin matakai domin dakile yaduwar cutar sankarau a Najeriya, inda ta kafa cibiyoyin gwaji da killace masu cutar a jihohi shida da annobar ta fi kamari.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da cutar ke ƙara yaduwa tare da janyo asarar rayuka, inda rahotannin baya-bayan nan suka nuna cewa mutane 151 ne cutar ta hallaka, ciki har da yara ƙanana fiye da 60.
A cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar, hukumar ta bayyana cewa jihohin da aka fi mai da hankali wajen ɗaukar matakan gaggawa sun haɗa da Jigawa, Yobe, Gombe, Katsina, Kebbi da Sokoto.
Wannan na biyo bayan yadda aka lura da hauhawar yawan masu kamuwa da cutar a waɗannan sassan tun bayan barkewar cutar a farkon shekarar nan.
Rahoton hukumar ya nuna cewa daga cikin jihohi 23 da annobar ta bulla, mutane 1,826 ake tsammanin suna fama da cutar a halin yanzu.
Wannan adadi ya ƙara ɗaga hankalin hukumomin lafiya da sauran hukumomin da ke aiki da su wajen dakile cututtuka masu yaɗuwa.
A halin yanzu, NCDC na ci gaba da aiki tare da ma’aikatun lafiya na jihohi da ƙasa baki ɗaya, domin tabbatar da cewa an samar da isassun kayan gwaji, magunguna da cibiyoyin killacewa, tare da wayar da kai ga jama’a kan alamomin cutar da hanyoyin kariya daga kamuwa da ita.
Sankarau na ɗaya daga cikin cututtukan da ke da saurin yaduwa musamman a lokacin damina da lokacin sanyi, kuma yana buƙatar gaggawar kulawa domin hana yaduwar sa cikin al’umma.
Hukumar NCDC ta bukaci iyaye da masu kula da yara da su kasance masu lura da lafiyar ‘ya’yansu, tare da gaggauta kai su asibiti idan suka lura da alamomin cutar kamar zazzabi mai tsanani, ciwon kai, da kasala.