Mai martaba Sarki Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa kowamar sa makaranta yayi ne don karawa alumma kwarin gwaiwar daukar ilimi da mahimmanci.
Mai martaba Sarki muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne bayan da Hukumar jamiar Northwest ta sahalewa manema labarai daukar rahoto yana tsaka da daukar darasi, a cikin aji.
Da yake jawabi yace sama da shekaru masu yawa yana da burin karantar fannin sharia.
Wasu daga cikin daliban jami’ar da suka kasance abokan karatun mai martaba sarkin na Kano a wannan tsangaya, sun bayyana wa Premier Radio, yadda suka rinski kansu bayan kasancewar sarkin a ajinsu.
Inda suka ce ganin Sarkin Kano a ajinsu ya sa sun ƙara samun ƙarfin gwiwa domin cigaba da neman ilimi.
Sarki Muhammadu Sunusi ya ce komawar sa wannan karatu, ba zai Hana shi tafiyar da ayyukan masarauta ba.
