Hukumar kare haƙƙin ɗan’adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kaddamar da bincike a hukumance kan zargin kisan ƙare-dangi da aka yi a birnin El-Fasher na Sudan a watan da ya gabata.
Yayin da aka soma wani taron gaggawa, shugaban hukumar Volker Turk ya fada wa taron cewa lamarin da ya faru abu ne da za a iya hasashen faruwarsa kuma a kauce masa.
Ya ce zalincin da aka yi a El-Fasher abin kunya ne ga kasashen duniya.
Volker Turk ya ce wajibi ne ƙasashen duniya su ɗauki mataki kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni da ke rura wutar yaƙin kuma su ke amfana da shi.
Ana zargin mayakan RSF din sun kashe aƙalla mutum 2,000.
