
Wani lauya mai suna Johnmary Chukwukasi Jideobi a Abuja ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya a Abuja (ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/2102/2025) don hana tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Goodluck Jonathan, tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ko wani zaɓe na gaba.
Ƙarar, wadda aka shigar ta sanya Jonathan a matsayin wanda ake ƙara na farko, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) a matsayin ta biyu, da kuma Babban Lauyan Gwamnati (AGF) a matsayin na uku.
Jideobi ya ce, Jonathan ya ƙare wa’adin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada a sashi na 137(3).
“Mutumin da aka rantsar da shi a matsayin Shugaban ƙasa don kammala wa’adin wani da aka zaɓa a matsayin Shugaban ƙasa, ba zai iya zama a wannan ofishin fiye da wa’adi ɗaya ba.
“Ya kammala wa’adin ‘Yar’Adua a matsayin wa’adi ɗaya, kuma zaɓen 2011 shine “wa’adi ɗaya” da aka yarda, saboda haka tsayawa takara a 2027 zai zama kamar wa’adi na uku kuma ya saba wa shekaru takwas na jimlar wa’adin”. In ji shi.
Lauya Jideobi ya yi gargadin cewa idan Jonathan ya ci zaɓen 2027 (ya shugabanci daga 2027–2031), hakan zai saba wa ikon tsarin mulki a sassan 1(1), 1(2), da 1(3).
Ƙarar ta samo asali ne daga rahotannin kafofin watsa labarai game da yuwuwar Jonathan na tsayawa takara, kodayake Jonathan bai bayyana a fili cewa zai tsaya a 2027 ba.
An rantsar da shi a ranar 6 ga Mayun shekara 2010, don kammala wa’adin marigayi Shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua kusan shekara ɗaya, sannan aka zaɓe shi kuma an rantsar da shi na cikakken wa’adi na shekaru huɗu a ranar 29 ga Mayu, 2011 2011 zuwa 2015.
Jideobi yana neman waɗannan yanke hukunci daga kotu cewa ta tabbatar Jonathan ba shi da damar tsayawa takara ko zama shugaban ƙasa, Sannan INEC ba ta da ikon karɓa ko buga sunan Jonathan a matsayin ɗan takara daga kowace jam’iyya.