Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Tukur Buratai, ya yi gargaɗi kan dogaro da sojoji wajen ayyukan tsaron cikin gida, yana mai cewa hakan na raunana ƙarfin ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a Kwalejin Tsaron Qasa da ke Abuja, yayin taron tunawa da sojojin da suka mutu.
Buratai ya kara da cewa yawan tura sojoji jihohi 36 na kasar da Babban Birnin Tarayya, na rage tasirin ’yan sanda da hukumomin leken asiri, waɗanda kundin tsarin mulki ya tanadar su jagoranci tsaron cikin gida.
“Kundin tsarin mulki ya fayyace a sarari aikin sojoji, wanda ya haɗa da kare ƙasa daga hare-haren waje, tsaron iyakoki, murkushe tayar da kayar baya, da kuma taimaka wa hukumomin farar hula idan buƙata ta taso,” in ji Buratai.
Haka zalika, Ministan Tsaro kuma tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su haɗa kai wajen dakile hanyoyin da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen safarar makamai, miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyakin haramtattu ta sufuri na cikin gida.
