Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan ta’addan da ke gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas da su ajiye makamansu, su miƙa wuya ga hukumomi, tare da rungumar zaman lafiya.
Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar APC da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Shugaban ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa na ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Ya kuma yi alƙawarin ceto ɗaliban da har yanzu ke hannun ’yan ta’adda, tare da yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Tinubu ya buƙaci masu rajistar zaɓe su karɓi katunan zaɓensu na dindindin (PVC), domin samun damar kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci al’ummar Borno da su goyi bayan sake zaɓen Tinubu domin yin wa’adi na biyu.
Shi kuwa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yaba da tallafin gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin tsaro, tare da yin kira da a dawo da ayyukan haƙo man fetur a yankin Arewa maso Gabas.
