Ma’aikatar Man fetur ta Iraqi ta yi wa kamfanonin Amurka tayin sayen ɗaya daga cikin yankunan kasar mai arzikin man fetur a duniya.
Matakin hakan na zuwa ne bayan rahotannin cewa kamfanin Lukoil na Rasha ya shafe shekaru ya na aiki a wurin.
Kamfanin ya sanar da ƙasar cewa ba zai iya ci gaba da aiki a rijiyar man ba, sakamakon takunkuman da Amurka ta lafta masa a watan Oktoba.
SERAP Ta Bukaci Tinubu Ya Hana Wike Rufe Ofisoshin Jakadanci kan biyan haraji
Karancin Man Fetur: Gwamnatin Mali ta sanar da rufe Makarantun kasar
Gwamnatin Trump ta kuma ƙaƙaba wa wani babban kamfanin mai na Rasha mai suna Rosneft takunkumi.
Wani mataki da ta kira ƙara matsin lambar tattalin arziƙi kan Rasha domin kawo ƙarshen yaƙin da ta ke yi a Ukraine.
