Wani matashi mai suna Umar Halilu Babatuwa ya rasa ransa sakamakon fadan daba tsakanin Kofar Nassarawa da Kofar Danagundi a jiya Lahadi a nan Kano.
A tattaunawar premier radio da yayan marigayin, Aliyu Halilu yace suna zaune ne a unguwar Danagundi kuma umar ya fita daga gida da karfe 10 na dare inda fitar tashi ba dadewa sai gashi an dawo fashi da sara da suka a jikin shi.
Aliyu Yace a daren suka tafi kaishi asibiti domin ceto ransa, sai dai sun hadu da yansanda a hanya amma yansandan suka kasa bada ko mutum daya ne a cikin su a kaishi asibitin. Yace ba wanda yasan dalilin shigowar yan daban yankinsu don haka suke bukatar gwamnati ta shiga ciki wajen nemo dalilin afkuwar lamarin.
