Masana’antar jiragen sama a Najeriya na fuskantar karin matsin lamba yayin da farashin man jiragen sama ke ci gaba da tashi a sassa daban daban a kasar nan.
mai magana da yawun kungiyar masu aikin jiragen sama ta kasa Farfesa Obiora Okonkwo, ya bayyana cewa a baya baya nan an sayar da man jiragen sama akan ₦1,000 duk lita, amma yanzu ya kai kimanin ₦1,800.
Valuejet Diele Damsa ya bayyana cewa kara kudin tikitin tafiye tafiye jirgin sama abun ne da ake bin tsare tsare kafin a kara.
Masana harkar sufurin sama sun gargadi cewa wannan karin kudin man na iya tilasta kamfanonin jiragen sama su kara farashin tikiti domin daidaita kudaden aiki.
Sun kara da cewa hakan na iya rage yawan mutanen da ke yin tafiye-tafiye ta jirgin sama, musamman wadanda tafiyarsu ba ta da matukar muhimmanci.
