
Kungiyar Dillalan Man fetur Ta Kasa (IPMAN) ta ce, za a samu saukin farashin man fetur matukar za a ci gaba da sayar da shi da Naira.
Hasashen hakan ya biyo bayan matakin da Matatar Dangote ta dauka na komawa sayar da man fetur da Naira, wanda ke kara ƙwarin gwiwar cewa farashin fetur zai sauka a faɗin Najeriya.

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da mai da Naira tsawon kwanaki 22, amma yanzu ta sanar da abokan hulɗarta cewa za ta rika sayar da litar mai a kan Naira 865, bayan rage N15 daga tsohon farashin Naira 880.
Mmatakin ya zo ne da nufin saukaka wa masu sayen mai da kuma rage nauyin farashin a gidajen mai.
A yayin zantawarsa da Premier Radio, sakataren kudi na kasa na IPMAN, Alhaji Musa Yahaya Maikifi, ya bayyana cewa matakin matatar Dangote zai yi tasiri wajen rage farashin man fetur a faɗin ƙasa.
Ya kuma ce, idan matatar ta yi ragi, dole ne masu sayen mai su ma su yi sauki, wanda hakan zai kai ga saukin farashi ga al’umma.
Wannan matakin na matatar Dangote ya jawo hankalin jama’a da masu ruwa da tsaki kan yadda zai taimaka wajen rage farashin man fetur a Najeriya.
IPMAN ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin man fetur da su bi wannan tsari domin saukaka wa al’umma.