
Fadar shugaban kasa ta kalubalanci ikirarin da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi, na caccakar gwamnatin Bola Tinubu kan abin da ya kira watsi da yankin arewacin Najeriya.
Kwankwaso ya ce shugaba Bola Tinubu, ya fi mayar da hankali kan gina kudancin ƙasarta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen taron shawarwari na masu ruwa da tsaki a jihar Kano na 2025 – wanda aka gudanar da yammacin Alhamis ɗin nan.
A wata sanarwa da fadar ta bakin mai bawa shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai Sunday Dare, ya fitar ya musanta ikirarin na Sanata Kwankwaso.
Dare ya ce Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu na bakin kokokarinta wajan gudanar da ayyuka a yankin arewacin Najeriya.