Gwamnatin Tarayya tare da Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Ƙasa (ASUU) sun rattaɓa hannu kan sabuwar yarjejeniya da nufin inganta tsarin ilimin jami’o’in ƙasar nan, tare da kawo ƙarshen yawan yajin aikin da ke durƙusar da harkokin karatu.
ASUU ta bayyana cewa sabuwar yarjejeniyar da aka cimma za ta taimaka matuƙa wajen bunƙasa harkokin koyo da koyarwa a jami’o’in.
Ƙungiyar ta ce yarjejeniyar za ta rage yawan yajin aiki, waɗanda a baya suka samo asali ne daga gazawar gwamnati wajen cika alkawurran da aka cimma tun yarjejeniyar shekarar 2009.
A ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar, an tanadi muhimman alawus-alawus ga malamai, da suka haɗa da kuɗaɗen wallafa mujallu na ilimi, halartar taruka, kuɗaden intanet, zama membobin ƙungiyoyin ilimi, da kuma alawus na sayen littattafai.
Ministan Ilimi na Ƙasa, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa an sake nazarin albashi da alawus na malaman bisa sabon tsarin yarjejeniyar.
Ya ce sabon tsarin biyan albashin zai fara aiki ne daga watan Janairu na shekarar 2026.
