
Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani mai zafi ga kalaman Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, bayan da ya caccaki nade-naden da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kwanan nan, yana mai cewa suna buƙatar sake nazari da tuntuba.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X a yammacin Talata, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana sukar nade-naden na Ndume a matsayin rashin hangen nesa da fahimtar cikakken yanayi.
“Sanata Ndume ya mayar da hankali ne kan abubuwan da bai da masaniya a cikinsu, maimakon ya karkata akalarsa zuwa manyan matsalolin da ke fuskantar yankin sa da ƙasa baki ɗaya.” In ji shi.
Onanuga ya caccaki Ndume da kasa sukar nade-naden da suka shafi ‘yan uwansa da shugaba Tinubu yayi a kwanan nan.
“Sanatan bai ce komai ba lokacin da mutum biyu da ke da alaka da shi suka samu manyan mukamai a cikin kamfanin man fetur na ƙasa NNPC.” In ji shi.
Onanuga ya shawarci Ndume da ya mai da hankali kan aikinsa a majalisa, yana mai cewa hakan ne zai ba shi girma da mutunci a idon jama’a fiye da sukar da ba ta da tushe ko makama.