’Yan bindiga a yankunan da ke tsakanin jihohin Kano da Katsina sun kakaba haraji ga manoma, inda aka tilasta musu biyan har zuwa ₦50,000 a kowace eka kafin su girbe amfanin gonarsu, musamman manoman rake.
Rahoton jaridar The Guardian ya bayyana cewa ’yan bindigar sun kafa sansanoni a Dajin Rugu da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, da kuma Dajin Falgore a karamar hukumar Doguwa a jihar Kano.
Daga wadannan wurare ne suke karɓar haraji tare da yi wa manoman barazana.
A cewar rahoton, manoman da suka ƙi biyan kudin harajin na fuskantar barazanar lalata amfanin gonarsu ko kai musu hari, lamarin da ya tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu domin tsira da rayukansu.
Rahoton ya kuma nuna cewa galibin wadanda matsalar ta fi shafa su ne manoman rake.
