
Daga Khalil Ibrahim Yaro
A Karon Farko Sardaunan Kano kuma tsohon gwamnan jihar Mallam Ibrahim Shekarau ya yi mubaya’a ga Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II.
Tsohon gwamnan ya yi mubayar’ar ne ga sarkin a Filin Jirgin Sama na malam Aminu Kano a ranar Asabar a dai dai lokacin da Sarkin ya je domin tafiya Lagos, a cewar wakilinmu.
Hakan kuma ta tabbata ne a wani hoto da aka dauka da sarkin na zaune kan kujera, sardaunan kuma na zaune a gabansa a kasa yana gaisuwa.
Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ne ya nada tsohon gwamnan a matsayin Sardaunan Kano a cikin watan Nuwanaban 2009.
Shekara Guda kenan da nada Sarkin Kano Muhammad Sanusi ll a matsayin Sarkin Kano amma ba a taba ganin Sardaunan Kano a Fadar Sarki ba da nufin gaisuwa ko ziyara.