Mai rikon aikin horarwa na Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC Rabi”u Tata, ya bayyana kwarin gwiwa ta samun nasara a kan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a wasan da zasu fafata.
Rabi”u Tata, a zantawarsa da Premier Radio ya ce kwarewar da ya ke da ita a gasar cin kofin kalubale, za ta taimaka masa ya iya jagorantar Barau FC ta yi nasara a kan Kano Pillars.
Barau FC za ta kece raini da Kano Pillars a gasar cin kofin kalubale ta kasa a matakin jihar Kano, wasan da zai gudana a ranar Lahadi 23 ga Fabrairu a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata da karfe 4 na yamma.
Rabi”u Tata a kakar wasannin da ta gabata, ya jagoranci Kebbi United ta kai wasan kusa da karshe a gasar cin kofin kalubale ta kasa President Federation Cup, sai dai a yanzu yana fatan ya lashe kofin da kungiyar Barau FC da yake jagoranta.
Rabi”u Tata ya bayyana Kano Pillars na da damar da zata iya lashe gasar, amma yace kwarewar da yake da ita za ta taimaka masa ya jagoranci Barau FC lashe gasar ta bana.
Idan ba a mantaba, Pillars ce ta lashe gasar a shekarar da ta gabata a matakin jihar Kano, kuma ta taba lashe gasar ta President Federation Cup a shekarar 2019 bayan do ke Niger Tournadoes a wasan karshe da ci 4-3 a bugun Penareti.
Ana saran wasan na yau zai dauki hankalin masu bibiyar kwallon kafa a matakin jihar Kano domin kallon yadda Kano Pillars mai buga gasar NFPL da Barau FC mai buga gasar NNL zasu kece raini da junansu a yammacin yau Lahadi a Sani Abacha Stadium da karfe 4 na yamma.
