
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai samu nasarar sake lashe kujerar shugaban kasa a zaben 2027 ba.
Da yake magana a wani shiri na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya bayyana cewa a mafi kyau ma, Tinubu zai zo ne na uku a jerin masu neman kujerar shugabancin Najeriya.
Ya kuma yi hasashen cewa akwai yiyuwar zaben ba zai kare a zagaye na farko ba, inda za a je zagaye na biyu ko kuma runoff, sai dai a cewarsa Shugaba Tinubu ba zai ma kai ga shiga wannan zagaye na biyu ba.
El-Rufai ya ce mutane da dama da ke kusa da Shugaban kasa na masa karya ne, suna yaudarar sa da cewa zai samu nasara saboda kudin gwamnati ko tasirin gwamnati, amma a gaskiya lamarin ya sha bamban.
Tsohon gwamnan ya kuma kara da cewa, shi da kansa ya yi aiki tukuru wajen yakin neman zaben Tinubu a 2023, amma hakan bai sa Tinubun ya samu nasara a Kaduna ba, haka kuma Tinubu bai ci jiharsa ta Legas ba duk da cewa gwamnan dan jam’iyyarsa ne.
Har yanzu babu wani martani daga fadar shugaban kasa dangane da wadannan kalamai na Malam El-Rufai.
Tsohon Gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ce ta dauki ’yan daba domin tarwatsa wani taron jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da aka gudanar a ranar Asabar.
El-Rufai ya yi wannan magana ne a cikin shirin Sunday Politics na gidan talbijin na Channels. A cewarsa, ikirarin rundunar ’yan sanda ta Kaduna cewa jam’iyyar ADC ce ta gayyato ’yan daban ba gaskiya ba ne.
Ya ce jami’an ’yan sanda sun kasance a wurin lokacin da abin ya faru, amma duk da haka an bai wa ’yan daban kariya. Ya kara da cewa waɗannan ’yan daba gwamnati ce ta dauko su.
El-Rufai ya kuma bayyana cewa ya taba mika korafi ga Sufeto Janar na ’Yan Sanda a baya kan wasu jami’an ’yan sanda a Kaduna da ake amfani da su wajen tsoratar da masu adawa da gwamnati.
Ya kara da cewa zai sake mika korafi ga babban sufeton da Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda (PSC), yana mai gargadi cewa amfani da jami’an tsaro wajen kare masu haddasa tashin hankali babbar barazana ce ga dimokuradiyyar Najeriya.